Faransa

Ana gudanar da bukin ranar ‘yanci a kasar Faransa

Al’ummar kasar Faransa na gudanar da bukukuwan ranar ‘yancin Kai, bukukuwan da a Bana aka gayyaci manyan Baki da suka hada har da sojojin kasar Algeria domin gudanar da fareti na musamman

Talla

Bukukuwan dai na a matsayin tunawa ne da ranar 14 ga watan Yulin shekarar 1789, lokacin da al’ummar Faransa suka samu nasarar kawo karshen mulkin gidan sarautar kasar.

Samun wannan nasara na a matsayin tubali na farko na dora Faransa akan turbar ‘yanci da Dimokuradiyya, duk da cewa an zubar da jinni sosai kafin samun wannan galaba.

A rana irin ta yau, kusan ana iya cewa mafi yawan Faransawa a duk inda suke a Duniya, kan koma gida domin gudanar da wadannan bukukuwa a cikin iyalansu, yayin da illahirin jami’an tsaro kasar kama daga sojoji har zuwa ‘yan sanda da dai sauransu, kan gudanar da fareti a shahrarren dandalin nan na kusa da fadar shugaban kasa wato Champs Elysees a birnin Paris.

Sai dai wani abu a game da faretin na bana, shi ne yadda aka gayyaci sojin Algeria, wato karo na farko a cikin tarihi, yayin da a can Algeria, al’umma ke adawa da hakan, saboda sabanin da ke tsakanin kasashen biyu tun lokacin mulkin mallaka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.