Rasha-Ukraine

Amurka da Turai sun tsaurara wa Rasha takunkumi

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama REUTERS/Kevin Lamarque

Kasar Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai sun tsaurara wa kasar Rasha takunkumi saboda yadda ta ke ruwa da tsaki a rikicin Ukraine, wannan na zuwa ne kuma a yayin da ‘Yan tawayen Ukraine da ke kishin Rasha suka ce zasu tattauna da masu shiga tsakani.

Talla

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi gargadin cewa zai mayar da martani akan Amurka.
Takunkumin Amurka ya shafi kamfanonin hada hadar kudi da makamashi na Rasha.

‘Yan Tawayen kasar Ukraine sun ce zasu tattauna da masu shiga tsakani don kulla yarjejeniyar zaman lafiya a kasar a yau Alhamis. Andrei Purgin, mataimakin Firaministan Donetsk da ya ayyana cin gashin kai yace da yammaci ne za’a yi tattaunawar.

Kokarin irin wannan tattaunawar a baya dai bai haifar da da mai ido ba.

Wannan na zuwa ne a yayin da ake musayar kalamu tsakanin Rasha da Ukraine, inda a yau Alhamis Ukraine tace wani Jirgin saman Rasha ya kakkabo jirginta a gabacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.