Faransa-Isra'ila

Gaza: An haramta zanga-zangar adawa da Isra’ila a Paris

Zanga-zangar Adawa da Isra'ila a Paris
Zanga-zangar Adawa da Isra'ila a Paris

Mahukuntan kasar Faransa sun haramta gudanar da zanga-zangar kin jinin Isra’ila a sassan yankunan kasar bayan zanga-zangar ta rikide zuwa rikici. ‘Yan Sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa gungun masu zanga-zangar da suka yi amfani da kwalabe da duwatsu suna jifar su a birnin Paris.

Talla

‘Yan sandan Faransa sun ce sun cafke kimanin mutane 40, kuma sun ce mutane 17 suka jikkata.

Firaministan Faransa Manuel Valls ya goyi bayan a haramta zanga-zangar, saboda fargabar za’a iya kai wa Yahudawa hari a birnin Paris.

Kasar Faransa ita ke da yawan al’ummar musulmi a nahiyar Turai da kuma Al’ummar Yahudawa da yawansu ya kai 500,000.

Dubban mutane ne suka shiga zanga zangar adawa da yadda Israila ke ci gaba da kashe Falasdinawa a birnin London.

Masu zanga zangar a London sun bayyana samun goyan bayan mutane 200,000 wadanda suka nuna bacin ransu a ofishin jakadancin Isra’ila da kuma fadar Firaminstan David Cameron.

An kwashe kwanaki 13 Isra'ila na kai hare hare a Zirin Gaza inda kimanin mutane 420 aka ruwaito sun mutu, da kuma Yahudawa guda biyu da suka mutu a hare haren rokoki da Hamas ke cilla wa zuwa Isra'ila

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.