Australia

Ana gudanar da taron masana kan Cutar Kanjamau a Australia

siklusair.com

Ana ci gaba da gudanar da taron masana kan yaki da cutar Aids ko Sida a birnin Melbourne na kasar Australia. Alkaluma sun bayana cewa an soma samu nasara wajen yaki da cutar duk da yake da sauran aiki daga bangaren hukumomin  

Talla

Baban taro karo na 20 da ya hada masana da kungiyoyin da ke yakin da cutar aids ko Sida daga kasashen duniya da ke gudana a kasar Australia, zai maida hankali ne wajen gano hanyoyin da suka dace domin yakar cutar nan ta Aids ko kuma Sida.

Wannan Cutar da bicinke ya gano cewa sama da mutane milliyan 35 a Duniya ke dauke da ita, sama da masana 12.000 ne daga kasashe 200 suka samu halarta wanan taro da ke zuwa a dai-dai lokacin da kasashe ke cikin juyayi mutuwar wasu daga cikin mahalarta wanan taro da suka mutun a cikin hadari jirgin saman nan na kasar Malaysiya da aka kakabo daga sararin samaniyar kasar Ukraine.

A ranar farko, sanarwa da ta fito daga zauren taron ta bayyana yadda aka samun ci gaba wajen yaki da wanan cuta duk da yake da sauran aiki wajen fadakar da al’umar dangane da hanyoyin da suka dace wajen kiyaye kamuwa da cutar, ta yadda za’a rinka ba da kulawa zuwa wadan da suka kamu da ita cutar.

Rahotanni na nuna yadda aka samu ci gaba a gabascin Nahiyar turai da tsakiyar Asiya, da ma Arewaci Nahiyar Afruka wajen yaki da kamuwa da wanan cuta, yayin da kusan mutane milliyan 14 ne ke samu kulawa daga jami’an kiwo lafiya a sassa daban-daban.

Alkaluma sun bayana cewa kusan mutane milliyan 28 ne ke bukatar taimako, da ma kulawa, a yyain da kusan kashi 44 na Matasa ne daga kudanci sahara ke fama da ita.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.