Faransa-Jamus

Shekaru 100 da barkewar Yakin Duniya na Daya

Sojan Faransa a yakin Duniya na Biyu
Sojan Faransa a yakin Duniya na Biyu Göttert/ German Federal Archives/ Wikimedia CC

A jiya lahadi ne aka soma gudanar a bukukuwan cika shekaru dari daya cur da barkewar yakin Duniya na Daya, wato ranar da Jamus ta kaddamar da yaki a kan kasar Faransa.  

Talla

A ranar farko ta soma wadannan bukukuwa, shugaba Francois Hollande na Faransa da takwaransa na kasar Jamus Joachim Gauck, sun gudanar da addu’o’i na musamman a wata makabarta da aka binne sojoji sama da dubu 30 wadanda suka hallaka a lokacin da dakarun kasashen biyu ke kokarin kwace ikon garin Hartmanswillerkofp da a halin yanzu ke cikin Faransa.

Daga bisani shugabannin biyu sun kaddamar da aikin gina wata katafariyar cibiyar ajiye kayayyakin tarihi dangane da wannan yaki, wadda ake fatar budewa a shekara ta 2017.

A yau litinin kuwa, shugabannin biyu za su isa birnin Liege na kasar Belgium, inda za su hadu da shugannin wasu kasashen Turai akalla 20 da ke halarta bukukuwan tunawa da ranar 14 ga watan Agustan 1914 ranar da sojojin Jamus suka mamaye kasar ta Belgium.

Yakin Duniya na Daya wanda ya share tsawon shekaru 4 ana fafata daga shekarar 1914 zuwa 1918, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da milyan 10, yayin da aka raunata wasu fiye da milyan 20.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.