Faransa

Dokar samar da daidaito tsakanin maza da mata a Faransa

Shugaban Faransa Francois Hollande
Shugaban Faransa Francois Hollande REUTERS/Philippe Wojazer

Faransa ta soma aiki da sabuwar dokar da ke kara samar da daidaito tsakanin mata da maza a duk fadin kasar, bayan da shugaban Francois Hollande ya sanya wa dokar hannu.

Talla

Tun a ranar 23 ga watan Yulin da ya gabata ne Majalisar Dokokin kasar ta amince da dokar, kuma wasu daga cikin abubuwan da ta kunsa sun hada da tislata wa miji daukar hutun dole domin taya matarsa samar wa ‘yayansu tarbiyya.

Ministar kare hakkokin mata a Faransa Najat Vallaud-Belkacem, ta yi alkawalin cewa gwamnati za ta tsaya domin ganin an aiwatar da wannan sabuwar doka.

To sai dai akwai sabani tsakanin gwamnati da babbar jam’iyyar adawa ta UMP, dangane da wani sashe na dokar da ke bai wa mace damar zubar da ciki matukar dai ta shiga hali na damuwa sakamakon wani lamari na rayuwar duniya koda kuwa ba ya nasaba da daukar cikin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI