Faransa

Gwamnatin kasar Faransa za ta bayyana sunayen mambobin sabuwar Gwamnati

AFP PHOTO/Patrick Kovarik

Wani lokaci a yau Talata 26 ga Watan Agusta ne ake sa ran Hukumomi a kasar Faransa za su kafa sabuwar gwamnati tare da bayyana sunayen mambobin Gwamnatin Firaiminista Manuel Valls. Sai dai kamar yadda za ku ji a wannan rahoto, tuni ministan kudin kasar ya ce ba zai shiga sabuwar gwamnatin da ake shirin kafawa ba

Talla

Shugaban kasar Faransa Fracios Hollande ne ya bukaci Firaiministan kasar ta Faransa Manuel Valls, ya bayyana sunayen mambobin Majalisar zartaswa ta sabuwar gwamnatin kasar, bayan da shugaban kasar ya yiwa gwamnatinsa garabawul.

Ministan harkokin tattalin arzikin kasar ta Faransa Arnaud Montebourg da kansa ne ya sanar da cewa ba zai karbi mukami a sabuwar gwamnatin da ake shirin kafawa a marecen talata ba.

Ya ce ina mai bugun gaban cewar a nawa bangare na sauke nauyin da aka dora min, kuma a wannan lokaci nake sanar da firaiminista cewa idan dai yana ganin cewa na kaucewa manufofin gwamnatin da yake jagoranta, to zai fi kyau in kasance a cikin ‘yanci, kuma tuni ya amince da hakan.

Sai dai ra’ayoyin sun sha bam-bam a game da yadda ‘yan siyasar ke kallon wannan mataki da ministan kudin ya dauka.

Luc Carnivaunas dan jami’yyar PS mai mulkin kasar ta Faransa, ya bayyana matukar mamakinsa game da murabus din da ministan tattalin arzikin kasar ya yi.

Shima dai Aurnaud Montebourg ya amince ya karbi wannan mukami ne alhali yana da cikakkiyar masaniya a game da manyan manufofin gwamnatin Manuel Valls, amma kuma ya karbi wannan matsayi a gwamnatin da aka kafa washe garin kammala zaben kananan hukumomi.

Amma jam’iyyar adawa ta UMP ta bayyana cewa murabus da ministan kudi ya yi, ta bakin wani babban jami’inta Eric Ciotti, wanda ya tabbatar da cewa a yanzu dole ne a kira zabe domin gwamantin Hollande ta rasa rinjayenta.

Ya ce wadanda ke karangar mulki sun rasa rinjaye da suke da shi, kuma ba ya zaton cewa gwamnatin da jam’iyyar ‘yan gurguzu ke jagoranta za ta ci gaba da wanzuwa, abinda ya rage mata kawai, ta kira zaben gaggawa domin dawo da matsayinta wajen al’umma.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI