Hungary

Hungry zata samar da hanyar sufuri ta zamani tsakaninta da Iran

eurotrib.com

Hukumomi a Kasar Hungary sun sanar da cewar nan bada jimawa ba za su kaddamara da jirgin Kasa mai tsananin gudu da zai fara safara tsakanin kasar da birnin Tehran na kasar Iran

Talla

Wannan ya biyo ne bayan wasu matakai na sassaucin ra’ayi da kasar ta Iran ta bayyana wa duniya ta dauka, yanzu haka kasar Hungary ta bayyana farin cikin ta, inda ta ce ya kamata su marawa Iran baya kuma hanyar yin hankan shine na fito da hanyar sufurin jiragen kasa na zamani, a cewar Marcella Beke shugabar kanfanin jiragen kasa na kasar ta Hungry.

Jirgin wanda aka yiwa kira irin ta zamani ya kunshi duk wasu kayyayakin more rayuwa, a yayin da matafiyi ke balaguro acikin sa.

Jirgin dai zai fara kai-komo a tsakanin kassahen biyu, a tafiyar da zai rinka kwashe tsawon makwanni biyu daga kasar ta Hungary tare da ratsa kasashen Romania da Bulgaria da Turkiya kafin ya shiga birnin Shiraz inda zai yada zango a Tehran babban birnin kasar ta Iran, akalla fasinjoji 70 da suka kunshi ‘yan asalin kasar Britaniya da Australia ne zasu kaddamar da jirgin a karon farko.

Ana sa ran ganin irin wannan kasaitatcen bulaguron ne akalla sau biyar a shekara mai zuwa kamar yadda shugabar hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta kasar ta sanar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI