Isa ga babban shafi
Amurka-Isra'ila

Amurka ta gayawa Isra’ila ta daina kwace Gonakin Falasdinawa

dangerouscreation.com

Kasar Amurka ta roki Gwamnatin Isra’ila da ta sauya matsayin ta kan shirin kwace wani sashe na Gonakin Inabi da al’ummar Falasdinawa suka dogara a kansu a Gabar yamma ga Kogin Jordan wato a Bethlehem

Talla

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta ce wannan matakin kamar duk wani matakin mamaye filayen Falasdinawa da Isra’ila ke yi, koma-baya ne ga shirin warware rikicin Gabas ta Tsakiya da kuma samun kasashe biyu a yankin.

Isra’ila dai ta sanar da shirin kwace fili mai girman Eka 400 saboda an kashe matasa Yahudawa uku, abinda ya haifar da yakin da aka kwashe kwanaki 50 anayi.
Isra’ila dai ta sha tofin Allah tsine daga sassan Duniya daban-daban kan yanda ta yi ta kisan Falasdinawa a yakin da take da kungiyar Hamas.

Harma mutane da daman a ganin cewar Isra’ila ba wata fama ta yi ba don ta yi fada da kungiya guda daga cikin kungiyoyin al’ummar Falasdinu a matsayinta na kasar da ke bugun Gaba da karfin Soji da kumakarfin tattalin arziki a yankin gabas ta tsakiya.

Hadin kan da aka samu tsakanin kungiyoyin Hamas da Fatah a baya ne dai ya tada hankalin kasar Isra’ila mai ganin cewar hakan ka iya zame mata babbar Barazana a kokarin ci gaba da rike kambinta a yankin na Larabawa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.