Isa ga babban shafi
Ingila

Birtaniya ta kaddamar da yaki da ta'addanci

Firaministan Kasar Birtaniya, David Cameron
Firaministan Kasar Birtaniya, David Cameron REUTERS/Luke MacGregor

Gwamnatin kasar Birtaniya ta dauki matakai akan ‘Yan kasarta da ke shirin shiga yaki a kasashen Syria da Iraqi tare da daukar matakai daga barazanar ‘yan asalin kasar wadanda suka dawo daga yaki a kasashen.

Talla

Firaministan Birtaniya David Cameron ya ce gwamnatinsa za ta dauki tsauraran matakai akan masu shirin shiga yaki da kuma haramtawa ‘Yan kasar masu kama da mayakan da suka fito yaki, shiga Birtaniya.

Matakan kuma sun hada da kwace fasfo na wadanda ke shirin zuwa Syria da Iraqi da tsaurara bincike a filayen jirage don dakile kwararan mayaka da ke dawo wa daga Yaki a kasashen.

Firaiministan kuma ya zayyana matakan ne a zauren Majalisa tare da bayyana cewa matakan sun zama dole idan ba haka ba Birtaniya na iya fuskantar hari anan gaba.

Yanzu haka kuma gwamnatin David Cameron ta kaddamar da yaki ne akan ‘Yan ta’adda.

‘Yan asalin Birtaniya kimanin 500 ne aka kiyasta sun tafi Syria da Iraqi kasashen da ke fama da Mayakan ISIS da ke gwagwarmayar shinfida sabuwar Daula.

Yanzu haka kuma cikinsu akwai kimanin 69 da ‘Yan sandan kasar suka cafke da ake zargi sun dawo yaki daga Syria.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.