Birtaniya

Karuwanci da cinikin miyagun kwayoyi na taimakawa tattalin arzikin kasar Birtaniya

en.wikipedia.org

Wani rahoto daga ma’aikatar kididdigar tattalin arziki na kasar Birtaniya na cewa ayyukan ashsha da suka hada da safarar miyagun kwayoyi da karuwanci na taimakawa kasar wajen samar da makudan kudade ga tattalin arzikin kasar 

Talla

A cewar Ofishin kididdigar tattalin arzikin Birtaniya, a Baara kawai safarar miyagun kwayoyi da karuwanci a fadin Birtaniya sun samarda kudaden shiga da suka kusa Fam biliyan 9, kwatankwacin Euro biliyan 11 ko kuma Dollan Amirka biliyan 14.

Kamar yadda wata mai Magana da yawun ofishin ke shaidawa kamfanin Dillancin labaran Faransa AFP, cewa alkaluman kididdigar na daga cikin sabbin tsare-tsaren auna karfin tattalin arziki da ake amfani da shi a kasashen turai.

Bayanin na cewa ta fannin su Barasa da safarar Sigari, akwai nasu kididdigar da akayi daban, kuma su ma suna taimakawa ga samar da kudaden shiga.

Kasar Spain, tun a farkon wannan shekarar take cewa kazaman ayyukan ashsha kamar su mu’amula da miyagun kwayoyi da karuwanci, sun sa kasar ta sami kudaden da suka haura Euro biliyan 9, ko Dollan Amirka kusan biliyan 12 a shekara ta 2010.

Ofishin kididdigar karfin tattalin arzikin na turai ya dibawa kasashen kungiyar zuwa jiya Talata kowacce ta gabatarwa Duniya bayanai irin haka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.