Faransa-Jamus

Jamus da Faransa na hararar juna kan matsalar tattalin arziki

newsroom.iza.org

Matsalar tabarbarewar tatallin arziki da ke ci gaba da addabar yankin Nahiyar Turai, ta yi sanadiyar raunin alakan tsakanin kasar Faransa da Jamus musamman ta fannin hadin gwiwa, kan mallakar wani kamfanin kera motoci. Kamfanin dai ya bada gudunmawa ta tsawon shekaru wajen bunkasa tattalin arzikin nahiyar Turai

Talla

Masana harkokin tattalin arziki sun bayyana cewa, wannan alakar da ke tsakanin kasashen Biyu, ba lallai ba ne ta dawo daidai matukar kasar faransa ba ta inganta hanyoyin karfafa tattalin arzikinta ba, yayin da masanan ke nuna cewar, alakar na iya dawowa kuma, lura da cewar kasar faransa na gaba dangane da siyasar harkokin waje, duk da cewa kasar jamus na jan ragwama wajan karfin tattalin arziki a nahiyar Turai.

kasar Jamus dai ta dan samu raunin tattalin arziki, amma hakan bai haifar da matsalar rashin aiki ba, sabanin faransa inda yanzu haka, ke fafutukar neman magance rashin aikin yi tsakanin matasa.

Lamarin dai ya haifar da sabani, yayin da dayan bangaren kuma kasar Jamus ta ce faransa ce za ta yi tunanin yadda za’a sasanta, duk da cewa shugabannin kasashen biyu na ci gaba da kai wa juna ziyara,

Firministan kasar faransa, Manuel Valls dai ya kai ziyara a birnin Berlin na kasar Jamus, yayin da shi kuma, Ministan harkokin wajen kasar Jamus, Frank Walter ya ziyarci birnin paris na Faransa, amma wannan sabanin na cigaba da wanzuwa a tsakaninsu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.