Brazil

Sakamakon farko a zaben Brazil

Shugabar kasar Brazil, Dilma Roussef
Shugabar kasar Brazil, Dilma Roussef REUTERS/Paulo Whitaker

Hukumar zabe a Brazil ta futar da sakamakon zaben ranar lahadi dake baiwa Shugabar kasar kuma yar takara Uwargida Dilma Roussef rijaye kuri’u da kusan kashi 41,48,yayi da dan takara Aecio Neves bangaren adawa, ya samu kashi 33,68 na kuri’u.

Talla

Dilma Rousseff ga dukkan alamu ake sa ran zata sake lashe zaben zagaye na biyu na ranar 26 ga wannan watan da muke cikin sa.
Hukumar zabe a kasar ta bayana cewa rashin samu rijaye daga kowane daga cikin yan takaran , dole sai an maimaita zaben ranar 26 ga wannan watan da muke ciki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.