Turai-Ebola

An tsaurara bincike a filayen Jiragen saman Turai kan Cutar Ebola

independent.ie

Kasashen Turai da suka hada da Amurka da Canada da Birtaniya da Faransa sun kara tsaurara bincike kan Cutar Ebola musamman a Filayen Jiragen sama, domin zakulo Pasinjoji masu kamuwa da Cutar

Talla

Wannan dai ya biyo ne bayan fargabar da ake kan Cutar musamman lura da yadda dan kasar Amurkar nan da ya kamu da cutar a bayan nan, ya mutu a birnin Texas, da kuma yanda yawan wadanda suka mutu sakamakon wannan Cutar ya doshi Dubu 4.

A kididdigar da Hukumar Lafiya ta Majalisar dunkin Duniya ta fitar dai akalla mutane Dubu 8 da doriya ne suka kamu da ita, a yayin da Dubu 3 da 865 kuma suka mutu.

A halin yanzu ma an kai mutane 2 a Assibitin birnin Los Angeles da Dallas na Amurka akan tuhumar su da kamuwa da Cutar.

A kasar Spain ma an ce an kebe mutane 5, a yayin da wasu masu dimbin yawa ke samun kulawar gaske bayan da wata Jami’ar kiyon lafiya a Madrid ta kamu da Cutar.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya yi kira ga kasashen Duniya da su taimaka domin abin yayi kamari.

Itama dai kasar Birtaniya na shirin tura Soji 750 da jami’an lafiya a Sierra lion kasar Liberia, domin marawa na Amurka baya duka don fada da Ebola.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.