Faransa

Gwamnatin Faransa na fuskantar suka

Martine Aubry,Magajiyar birni Lille da firaministan Faransa Manuel Valls
Martine Aubry,Magajiyar birni Lille da firaministan Faransa Manuel Valls REUTERS/Pascal Rossignol

Gawmnatin Firaminista Manuel Valls na Faransa na cigaba da shan suka, daga manyan jigajigan jam’iyyar Socialist dake mulkin kasar, kan kasawar da ta yi, wajen magance matsalolin tattalin arzikin da kasar ke fuskanta. Martine Aubry da ta tsaya takarar zaben fitar da dan takarar da zai wakilci jam’iyyar Socialiste a zaben da ya gabata, haka kuma yanzu itace magajiyar birnin Lille dake arwacin kasar Faransa, ta caccaki tsarin siyasar gwamnatin kasar. 

Talla

Magajiyar birni Lille ta bayyana wasu shawarwari ga babban zaman taron jam’iyya tareda bayana damuwa gani ta yada gwamnatin Valls ta kasa sai dai kuma ta ce lokaci bai kure ba wajen sake kai gwamnatin ga nasara .

Aubry a cikin ta ce tsarin siyasar tsawon shekaru 2 da gwamnatin ta socialiste ke bi kamar ko ina a kasashen turai ya ta’allaka ne wajen samar da ci gaba.
A kan haka ne kuma ta bayyana bukatar ganin an sake fasalta tsarin siyasar kudin da gwamnatin kasar ke bi, inda ta ce a cikin gauggawa ya kamata a samo hanyoyin da zasu bada damar daidaita fitar da kasar ta faransa daga dimbin matsalolin tattalin arziki da kasar ta samu kanta.
Martine Aubry ta bukaci a sake duba dubarun da hukumomin kasar Faransa suke bi wajen magance matsalar samar da kudi kafin lokaci ya kure masu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.