Fransa

Jam'iyyar masu ra'ayin rikau a Faransa FN na tunanin canza suna

Marine Le Pen, shugabar jam'iyyar FN a Faransa
Marine Le Pen, shugabar jam'iyyar FN a Faransa REUTERS/Benoit Tessier

Jam’iyyar Front National ta masu tsatsauran ra’ayin kishin kasa a Faransa, ta soma tunanin canza sunanta. To sai dai ba dukkanin magoya bayan jam’iyyar ne ke goyon bayan daukar wannan mataki ba.

Talla

Ko shakka babu dai akwai rabuwar kawuna a tsakanin ‘yayan jam’iyyar dangane da wannan mataki na canzawa FN suna, domin kuwa sanar da hakan ke da wuya, sai tsohon shugaban jam’iyyar Jean-Marie Le Pen ya fito a fusace a wannan litinin domin nuna rashin amincewarsa da hakan.

Kwanaki biyu kafin nan, ‘yarsa, wadda kuma ke shugabancin jam’iyyar yau shekaru uku kenan wadda kuma ake hasasashen cewa za ta iya zuwa zagaye na biyu na zaben shugabancin kasar a shekara ta 2017 wato Marine Le Pen, ta bayyana cewa lalle akwai bukatar zaunawa domin duba wannan batu na canza wa jam’iyyar suna.

Marine ta ce dole ne a bai wa magoya bayan jam’iyyar damar bayyana matsayinsu a game da yunkurin, wanda wasu ke ganin cewa ta hanyar canza suna, wadanda a can baya ke adawa da akidar jam’iyyar, za su iya jefa mata kuri’u a zabe mai zuwa.

Ita dai wannan jam’iyya, ta yi kauri suna ta fannin nuna kyama ga baki da kuma fafutukar ganin Faransa ta ci gaba da kasance ta Faransawa tsintsa, to sai dai matukar aka canza sunan daga Front National, to abin da zai biyo baya shi ne jam’iyyar za ta iya canza wasu daga cikin akidun da ke hana ta samun karbuwa daga wasu ‘yan kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.