Ukraine-Rasha

An soma tattaunawa tsakanin Ukraine da Rasha

Taron Kungiyar Turai da Shugabanin kasashen Rasha da Ukraine a Milan na kasar Italiya
Taron Kungiyar Turai da Shugabanin kasashen Rasha da Ukraine a Milan na kasar Italiya REUTERS/Ukrainian Presidential Press Service

Domin sake komawa aikin tura mata iskar Gaz daga Rasha Kasar Ukraine ta bukaci kasashen Turai da su karawa kasar bashin Euro Biliyan 2 domin biyan bashin Iskar Gaz da kasar Rasha ta bukaci ta biya nan da karshen watan October shekarar 2014. Hukumomin Rasha sun dakatar da aika Gaz a Ukraine cikin watan Yunin da ya gabata, kamar yadda kungiyar tarayyar turai ta Sanar

Talla

Wannan bukata da kasar ta Ukraine ta gabatar dai, yanzu haka an fara tattaunata tsakanin kungiyar ta tarayyar turai hukumar bayar da lamani ta duniya IMF da kuma ita kanta kasar Ukraine, kamar yadda kakakin hukumar zartarwar kungiyar ta turai Simon O Connor ya sanar, a yanyin da a birnin Bruxelles ake ci gaba da tattaunawa tsakanin Ukraine din da Rasha, domin samun tabbacin Rasha zata tura iskar Gaz din a Ukraine da sauran kasashen turai a wannan hunturu na bana.

Kwamitin zartarawar kungiyar ta tarayyar turai zai gabatar da wannan shawarar ga majalisar dokokin turai, da ta hada daukacin kasashe mambobin kungiyar su 27, kungiyar ta Turai zata ci gaba da bada goyan bayan ta zuwa kasar ta Ukraine in ji M O Connor
Tare da taimakon kungiyar ta tarayyar turai ne dai, Ukraine ke ci gaba da tattaunawa da Rasha, domin cimma yarjejeniya ta wucin gadi, da ta bukaci Ukraine ta biya bashin dalar Amruka biliyan 3,1, ga katafaren kamfanin Iskar Gaz din kasar Rasha Gazprom, inda zata biya biliyan 2 na Euro kafin nan da karshen watan October da muke ciki

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.