Faransa

Ana zargin wasu 'yan majalisar dokokin Faransa da kaucewa biyan haraji

Shugaban Faransa, François Hollande
Shugaban Faransa, François Hollande REUTERS/Stringer

‘Yan majalisar dikokin Fransa 60 ne ake zargi da fadawa cikin badakalar kaucewa biyan haraji a kasar. Wadanda ake zargi sun hada da masu matsala da tsarin biyan haraji, da kuma wadanda ke bi ta bayan fage su kai kudadensu a kasashen ketare Shekaru 2 ke nan tun bayan darewar jam’iyar Socialist kan karagar shugabancin kasar Fransa, ake ta kai ruwa rana tsakanin manyan jami’an gwamnatin kasar da Kotuna kan zargin kaucewa biyan haraji, Wannan sabon babi da aka bankado na ‘yan majalisar dokokin kasar kusan 60 da ake zargi da kaucewa biyan haraji a kasar, na matsayin babban abin kunya, da zai iya zub da mutuncin majalisar dokokin a idon Faransawa.Sunan Olivier Faure, kakakin jami’iyar Socialiste mai mulki ne kan gaba daga cikin ‘yan majalisar da ake zargi da kaucewa biyan harajinWannan sabon abin kunya da ya sake bullowa a inda ba a zata ba, daga bangaren masu yin dokoki, ya harzuka kafofin yada labaran Faransa, al’amarin da jaridar Canard Enchaîné ta kira sabuwar badakalar Thévenoud, wanda shine sunan tsohon sakataren gwamnatin kasar Faransa, da guguwar kaucewa biyan haraji ta yi awan gaba da shi Jerin sunayen ‘yan majalisar dake cikin wadannan kazaman ruwa za a sansu ne nan da watan Disamba, batun da zai zama abin mahawara da jita jita a kasar na tsawon makonni.