Faransa

'Yan sanda suna arangama da bakin haure a Faransa

Shugaban Faransa Francois Hollande
Shugaban Faransa Francois Hollande REUTERS/Christian Hartmann

Hukumomin kasar Faransa sun sanar da tura karin jami’an tsaro zuwa yankin Calais, bayan da wasu bakin haure dake kan hanyar zuwa Birtaniya suka mamaye wasu yankunan birni.Jiya Alhamis aka samu arrangama tsakani jami’an tsaron Faransa da wasu bakin haure a yankin Calais dake arewaci kasar.Rahotani daga yankin na cewa hukumomin sun sanar da aikewa da karin jami’an tsaro da za su taimakawa dakarun kwantar da tarzoma dake kokarin kilace wuraren da bakin suka mamaye.Bakin da akasarin su ‘yan kasar Eritreya ne, suna kan hanyarsu ta zuwa kasar Birtaniya ne.Tun da dadewa kasashen turai suka dau tsauraren matakai domin yaki da kwararar bakin haure zuwa yankin na turai.Bakin dake fama da karanci abinci na cikin hali kaka nikayi, yayin da kungiyoyin kare hakin bil Adam ke ci gaba da yin kira ga hukumomin wadanan kasashe, na ganin sun mutunta wadan bakin haure, dama kare su daga duk wata barrazana.