Ukraine

An kai wa shafin Intanet na hukumar zaben Ukraine hari

Akwatin Zabe a kasar Ukraine
Akwatin Zabe a kasar Ukraine REUTERS/Valentyn Ogirenk

‘Yan dandatso sun kai wa shafin intanet na hukumar zabe a kasar Ukraine hari a yau Assabar, Jajibirin babban zaben da za’a gudanar a cikin kasar. Wannan na zuwa ne bayan Shugabannin Ukraine sun yi kiran karshe na samun zaman lafiya ga al’ummar kasa da zasu jefa kuri’ar zaben Yan Majalisu da ake fatar zai bude kofar samun zaman lafiya a kasar.

Talla

Ukraine ta karyata rahoton da kafafofin yada labaran Rasha suka ruwaito cewa na’urar kidayar kuri’a ta samu matsala.

Rikici tsakanin Ukraine da Rasha da masu kishinta shi ne ya mamaye Ukraine.

A lokacin da ya ke jawabinsa na karshe kafin zaben, Shugaba Petro Poroshenko yace ko ba komi zasu zabi wadanda ke kishin Ukraine ma su da’awar Turai ba Rasha ba.

An shafe watanni ana tabka fada tsakanin Ukraine da ‘Yan tawaye masu kishin Rasha da ke son warewa daga kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.