Brazil

Dilma Roussef ta lashe zaben kasar Brazil

Shugabar kasar Brazil, Dilma Roussef
Shugabar kasar Brazil, Dilma Roussef REUTERS/Paulo Whitaker

Shuagabar Kasar Brazil Dilma Roussef ta bukaci yan kasar su hada kan su bayan samun nasarar zaben da ya raba kan al’ummar kasar, zagaye na biyu da kusan kashi 52. Yayin da take jawabi da daruruwan magoya bayan ta, Roussef tace a shirye take ta tattauna da yan kasar, wanda tace zai zama mafi muhimmanci a mulkin ta. 

Talla

Uwargida Dilama Roussef ta dau alkawarin zama shugaban kasa mafi inganci yanzu sabanin wa’adin ta na farko.
Tuni abokin takarar ta Aecio Neves ya buga mata waya inda ya taya ta murna.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.