Amurka

Za’a sabunta zanga-zangar kyamar gwamnati a Amurka

Protesto na California contra o arquivamento do caso de um policial que matou um jovem negro em Ferguson.
Protesto na California contra o arquivamento do caso de um policial que matou um jovem negro em Ferguson. REUTERS/Lucy Nicholson

A kasar Amurka wani lokaci a yau ne aka shirya gudanar da wata gagarumar zanga-zangar kara nunawa hukumomin kasar fa, ba’a aminta da yadda ‘yansanda fararen fata ke kisan gilla ga fararan Hula bakaken fata ba

Talla

An ce dai a wannan karon zanga-zangar za ta game biranen kasar da dama, kuma masu zanga-zangar na kokarin matsawa kasar Amurka lamba ne akan bukatar a dauki mataki ga yadda a baya-bayan nan ma’aikata suka kama nunawa bakaken Fatar kasar banbanci.

Idan ana iya tunawa a farkon watan jiya ne aka bada labarin kisan da wani dansanda farar fata ya yiwa wani farar Hula bakar fata, amma hukumomin kasar ta amurka basu yi komai akai ba.

Kasar Amurka dai na kan gaba ga gangamin kare ‘yancin bil’adama a Duniya, amma wannan al’amarin ya haifar da dari-darin da ake akan sahihancin adalcin da kasar Amurka ke cewar tana kwatantawa a tsakanin al’ummar kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.