Rasha zata rage yawan hatsin da ake fita dashi daga kasar

Le Premier ministre Dmitri Medvedev lors d'une interview à la télévision russe, le 10 décembre 2014.
Le Premier ministre Dmitri Medvedev lors d'une interview à la télévision russe, le 10 décembre 2014. AFP PHOTO / RIA-NOVOSTI / POOL / DMITRY ASTAKHOV

Gwamnatin kasar Rasha ta bayyana daukar wasu jerin matakai na saka shinge jami’an kostom domin rage fitar da hatsi da wasu kayayyakin cimaka daga kasar zuwa kasashen ketare. Kasar ta dauki wannan mataki ne da zummar rage hauhawar farashin cimakar da ake samu a kasuwanin cikin gida, sakamakon faduwar darajar kudin kasar na RubulMataimakin Fraiminista, Arkadi Dvokovitch ya tabbatar wa kamfanin dillancin kasar cewa, za a gabatarwa Fraiminista Dmitri Medvedev matakain cikin sa’oi 24, kafin ya sanya hannu a soma aiki da shi. Faduwar darajar kudin rubul na kasar ta Rasha ne ya haifar da tashin gwaron zabon da cimakar dangin hatsi ya yi a kasar ta Rasha, musaman alkama, duk da albarkar noman da aka samu a bana wanda ba a taba samun irinsa ba a kasar, inda aka kiyasta cewa kasar ta samu albarkar noma da yakai na kimanin ton miliyan 104 na hatsin Fraiminista Medvedev ya bayyana cewa, duk da sun samu albarkar noma a bana, amma faduwar darajar kudin Rubul ya haifar da tashin farashin cimakar a cikin kasuwannin cikin gida, inda yace suna da yalwatacen abinci a wannan kasar, amma dangane da hauhawan farashinsa dole ne, gwamnati ta dauki matakai na takaita fitar da shi a kasashen ketare domin karya darajarsa a cikin kasa.