Italiya

Jami’an Italiya sun yi kokarin ceto jirgin ruwan Bakin haure

Wasu bakin haure da aka kubutar a teku a Italiya
Wasu bakin haure da aka kubutar a teku a Italiya REUTERS/Stringer

Jami’an kula da jiragen ruwa a kasar Italiya sun nasarar ceto wani jirgin ruwa da ya samu matsala a tsakiyar teku shake da bakin haure kimanin 450 bayan sun yi nasarar ceto rayuwan bakin haure da dama a cikin kwanaki biyu da suka gabata.

Talla

jirgin ruwan ‘yan kasuwa ne shake da bakin haure 450, ya tsaya a tsakiya tekun kasar Italiya, sakamakon daukewar wuta daga injinan shi.

Yau juma’a rundunar sojan saman kasar tace an tura wani jirgin sama mai saukar ungulu, don ya kai wa matukan da za su kawo shi bakin ruwa.

Wani fashinja da ya iya sarrafa na’urar sadarwan jirgin ne ya sanar da jami’an da ke kula da ruwan kasar Italiya halin da suke ciki, inda su kuma suka bazama don kai dauki.

Jirgin mai suna Ezadeen, da aka yi wa rajista a kasar Saliyo, na da tsawon Mita 75 ko kafa 240, kuma ana amfani da shi ne wajen jigila tsakanin kasar Cyprus da gabar ruwan Sete dake kudancin Faransa.

Wannan lamarin na zuwa ne kwanaki kadan bayan hukumomin kasara ta Italiya sun kama wani jirgin ruwan da ya nufi gabar ruwan kasar, dauke da daruruwan bakin haure da suka fito daga arewacin nahiyar Africa.

Cikin wannan makon ma, an kama wani jirgin ruwan dauke da kusan mutane 770, da ya nufi Italiya daga kasar Turkiyya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.