Faransa

An samu raguwar kona motoci a bikin sabuwar shekara a Faransa

Motar da aka kona a Faransa a ranar bikin sabuwar shekara
Motar da aka kona a Faransa a ranar bikin sabuwar shekara France24

Gwamnatin Faransa tace an samu raguwar yawan adadin motocin da ake konewa a lokacin bikin sabuwar shekara da kashi 12 cikin 100 a cikin kasar. alkalumma sun nuna cewa a jajibirin sabuwar shekara an kone motoci 940 sabanin 1,067, da aka cinna wa wuta a shekarar da ta gabata.

Talla

Wannan dai wata al’ada ce da aka dade ana yi a Faransa.

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta kuma ce, an sami raguwar mutane da ake kamawa suna tayar da yamutsi a jajibirin sabuwar shekara.

Ma’aikatar tace an sami wannan ci gaban ne sakamakon matakan wayar da kan jama’a da jami’an tsaro suka dauka.

Mutane 308 aka cafke da ke tayar da yamutsi a lokacin bikin sabuwar shekara sabanin 322 da aka cafke a bara.

Gwamnatin Hollande dai ta kara inganta tsaro a lokacin bukukuwan Kirsemeti da sabuwar shekara, kodayake an samu mutuwar mutum guda da kuma mutane sama da 20 da suka samu rauni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.