Turkiya

Turkiya ta yadda a gina sabuwar Coci a Istanbul

Masallacin birnin  Istanbul, Turkiya.
Masallacin birnin Istanbul, Turkiya. Wikimedia commons

Gwamnatin Kasar Turkiya ta amince a gina Coci a karon farko a cikin kasar tun faduwar daular Ottoman a 1923, kamar yadda wata majiya daga fadar gwamnatin kasar ta tabbatarwa Kamfanin dillacin Labaran Faransa.

Talla

Wannan ne karon farko da za a samu ginin Coci tun kafa Jamhuriya a kasar Turkiya.

Mabiya addinin Kirista a Turkiya ne masu magana da harshen Syria za su gina Cocin a birnin Istanbul.

Akwai dai tsoffin Coci a Turkiya amma tun faduwar daular Ottoman babu wata sabuwar Coci da aka gina a cikin kasar mai yawan al’ummar Musulmi.

Wannan matakin kuma ya yi karo ga masu sukar gwamnatin Jam’iyyar AKP mai kishin addinin Islama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.