Jamus

An yi zanga-zangar kyamar Musulunci a Jamus

Kungiyar PEGIDA da ke jagorantar zanga-zangar kyamar addinin Musulunci a Jamus
Kungiyar PEGIDA da ke jagorantar zanga-zangar kyamar addinin Musulunci a Jamus REUTERS/Hannibal Hanschke

Akalla mutane dubu 18 ne suka shiga wata zanga-zangar nuna kyamar addinin musulunci a birnin Dresde da ke gabashin kasar Jamus. Wata kungiya ce mai suna PEGIDA ta jagoranci gangamin inda ta ce wasu na neman musuluntar da al’ummar Turai.

Talla

Sai dai masu wannan ra’ayi sun ci karo da turjiya daga wasu Jamusawa masu sassaucin ra’ayi da ke adawa da zanga-zangar a sauran biranen kasar.

Tun a watan Oktoba PEGIDA ke jagorantar zanga-zangar kyamar addinin Musulunci a Jamus duk da shugabar gwamnatin kasar Angela Merkel ta bukaci a dakatar da zanga-zangar.

Dubban masu zanga-zangar karo da Jamusawan da ke zanga-zangar kyamar Musulunci
Dubban masu zanga-zangar karo da Jamusawan da ke zanga-zangar kyamar Musulunci REUTERS/Wolfgang Rattay

Shugabannin Kiristoci da ‘Yan kasuwa da shugabannin siyasa a Jamus sun la’anci zanga-zangar da aka gudanar a biranen Berlin da Cologne da Stuttgart da Dresden.

Sai dai kuma masu zanga-zangar sun ci karo da dubban Jamusawa da suka kaddamar da zanga-zangar adawa da masu kyamar Musulunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.