Faransa

‘Yan bindiga sun kai hari a ginin Mujallar Charlie Hebdo

'Yan sanda a ofishin Mujallar Charlie Hebdo a birnin Paris
'Yan sanda a ofishin Mujallar Charlie Hebdo a birnin Paris REUTERS

Mahakuntan birnin Paris a Faransa sun tabbatar da mutuwar mutane 11 a wani hari da ‘yan bindiga suka kaddamar dauke da AK47 a ginin wata mujallar Charlie Hebdo da ta wallafa wani zane da aka danganta da Manzon Allah (SAW) a 2006.

Talla

Magajin garin birnin Paris, Bruno Julliard ya ce mutane shida 'Yan bindigar suka jikkata.

Yanzu haka ‘Yan sanda sun kaddamar da farautar ‘Yan bindigar guda biyu da suka shiga ginin ofishin Mujallar suna ruwan wuta.

Kasashen musulmi da dama sun yi Allah wadai da Jaridar wacce ta wallafa wani zane da ta danganta da Manzon Allah SAW a watan Fabrairun 2006.

A watan Nuwamban 2011 an taba kai wa Jaridar harin bom.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.