Faransa

Ana tausar Kai, Ciki na kaba. Wani dan Bindiga ya kaiwa 'yan sanda hari a Paris

AFP/Thomas Samson

Wani dan Bindiga dadi a birnin Paris na kasar Faransa ya kai wa 'yan sanda masu aikin bincike kan harin da aka kai wa Mujallar Charlie Hebdo da ya yi sanadin mutuwar mutane 12 ciki hadda 'yan jarida Takwas.  

Talla

A yayin da 'yan sanda a birnin Paris na kasar Faransa suka dukufa kan binciken wadanda ake zargi da kai wa Kamfanin Mujallar Charlie Hebdo hari, kwatsam wani dan Bindiga ya yi kukan Kura da Bindiga kan jami'an tsaro, inda ya jikkata 'yan sanda biyu.

Yanzu haka dai akwai rahotannin da ke nuna cewar Mace daya daga cikin jami'an tsaron da maharin ya jikkata ta rasa ranta, a yayin da wasu ke cikin halin tsaka mai wuya.

Matar dai na sanye ne da cikakkun Tufafin aiki masu kariya daga harin Bindiga, amma yanda maharin ya kasance kusa da ita ya sa Harsashen ya raunata ta.

An ce dai maharin ya ranta a cikin na Kare, kuma harin ya zo ne bayan wani harin da aka kaiwa Kamfanin Mujallar Charlie Hebdo, abinda ya kai jami'an tsaron kasar ga kaddamar da bincike don gano masu hannu ga harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.