Italiya

Berlusconi ya nemi sassauci

Tsohon Firaministan Italia, Silvio Berlusconi
Tsohon Firaministan Italia, Silvio Berlusconi REUTERS/Alessandro Bianchi/Files

Tsohon shugaban gwamnatin Italia Silvio Berlusconi ya roki a rage masa kwanaki 45 a cikin hukuncin tsawon shekara daya da aka yanke masa bayan samun sa da laifin kaucewa biyan haraji. A cikin watan agustan 2013 ne aka same shi da laifi, inda aka yanke masa hukuncin dauri na tsawon shekaru 4, kafin daga bisani a yafe masa shekaru uku, sannan kuma aka bukaci gudanar da aiki a wani gidan gajiyayyu na tsawon shekara daya.