Faransa

An fara zaman makoki na kwanaki 3 a kasar Faransa

REUTERS/Philippe Wojazer

Hukumomi a kasar Faransa sun ayyana yau Alhamis a matsayin ranar makoki kan kisan da aka yiwa mutane 12 a Kamfanin Jaridar Charlie Hebdo

Talla

Shugaba Francois Hollande na Faransa ne ya sanar da ware tsawon kwanaki uku na zaman makoki daga yau alhamis a duk fadin kasar, domin nuna alhini dangane da hari da aka kai wa ofishin mujallar Charlie Hebdo wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12.
Shugaba Hollande ya yi alkawalin mayar da zazzafan martani akan wadanda suka kai wannan hari, da yanzu haka jami’an tsaro k enema Ruwa-Jallo.
Hollande ya ce za mu yi nasara akan ‘yan ta’adda domin muna da karfin da za mu fayyace makomarmu, ba wanda ya isa ya canza mana manufofi.

Ba za mu taba mika wuya ga bukatun ‘yan ta‘adda ba, kuma rawar da muke takawa domin yaki da wannan matsala a sauran kasashe na Duniya, rawa ce da ba gudu ba ja da baya.

Faransa kasa ce da ke martaba ‘yancin fadar albarkacin baki saboda mun yarda da hakan, abun da nake bukata ga faransawa anan shi ne hadin kai da kuma nuna goyon baya ga yakin da muke yi da masu zazzafa ra’ayi.

Zan sake jaddadawa, ina kira a gare ku da kara bayar da hadin kai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.