Faransa

‘Yan sandan Faransa sun tsaurara tsaro

Jami'an tsaron Faransa a Paris
Jami'an tsaron Faransa a Paris REUTERS/Charles Platiau

Jami’an tsaro a Faransa sun tsaurara tsaro a arewacin birnin Paris inda wasu ‘Yan bindiga da aka bayyana ‘yan uwan juna ne suka kashe mutane 12 a harin da suka kai wa ofishin mujallar Charlie Hebdo da ta ci zarafin Musulmi. Yau da safiyar Alhamis wata ‘yan bindiga ya harbe wata ‘Yar sandan Faransa har lahira a kudancin Paris.

Talla

‘Yan sandan Faransa na musamman masu yaki da ta’addanci sun tsaurara tsaro a yakin arewacin Paris bayan an tsinci wata mota da ake zargin ta maharan ofishin Mujallar Charlie Hebdo ne da suka kai wa hari.

Bayanai na cewa maharan sun fara kai hari a wani gidan mai a arewacin Paris inda suka sace abinci da ruwan fetir tare da ruda wurin da karar harbin bindiga.

Masu bincike a faransa sun tsinci makamai a cikin motar, inda ake fargabar sun yi shirin kai wani hari ne.

Tun da safiyar yau Alhamis kuma wani dan bindiga ya harbe wata ‘Yar sanda har lahira a kudancin Paris tare da jikkata wani dan sanda.

Sai dai har yanzu babu wasu bayanai akan ko harin na yau Alhamis na da alaka da harin da aka kashe mutane 12 a ginin jaridar Charlie Hebdo a jiya Laraba.

Faransawa sun yi jimamin mutane 12 da ka kashe a harin mujallar a wani gangami da suka hada a Paris a yau Alhamis.

Mujallar tace za ta ci gaba da aikinta duk da harin da aka kai mata.

Yayin da wata jaridar Denmark da ta taba cin zarfin Musulmi ta ki wallafa labari akan harin na Charlie Hebdo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.