Faransa

An kashe maharan Charlie Hebdo

Manyan Zaratan Sojojin Faransa suna farautar Maharan Charlie Hebdo
Manyan Zaratan Sojojin Faransa suna farautar Maharan Charlie Hebdo REUTERS/Christian Hartmann

Jami’an tsaron Faransa sun kashe maharan Mujallar Charlie Hebdo guda biyu bayan sun fito suna harbin bindiga a gidan da suka yi garkuwa da mutane a yankin arewa maso gabashin birnin Paris. Tun lokacin da maharan suka kai hari a mujallar Charlie Hebdo, Jami’an Faransa suka kaddamar da farautarsu wadanda aka bayyana ‘yan uwan juna ne.

Talla

A yau Juma’a ne aka kashe Maharan bayan ‘Yan sanda sun abka ginin da suke buya.

Wannan al’amari dai ya ja hankalin duniya. Maharan sun kai harin ne domin mayar da martani ga Mujallar saboda ta ci zarafin addinin Islama.

Jami’an tsaro sun yi nasarar kubutar da mutane da dama da mahara suka yi garkuwa da su a wani babban shagon Yahudawa a Portes de Vincennes.

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya gudanar da wani taro da manyan jami’an tsaron kasar da kuma na gwamnatinsa, a daidai lokacin da kasar ke ci gaba da juyayin harin da aka kai a ranar laraba akan mujallar Charlie Hebdo, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12.

Jami’an tsaro sun killace wata unguwa da ke arewacin birinin Paris inda ‘yan bindigar da suka kai hari.

Zaratan sojoji akan rufin gine-gine da kuma jiragen sama masu saukar angulu ne suka zagaya sararin samaniyar unguwar da ke arewacin birnin Paris, inda aka tabbatar da cewa a can ne mutanen biyu da suka kai hari akan mujallar Charlie Hebdo suka ja daga dauke da nasu manyan makamai.

Jami’an tsaro sun kange dukkanin hanyoyin da ke shiga da kuma fita daga unguwar inda ake da manyan masana’antu a cikinta, yayin da sauran gidajen kalilan da jama’a ke rayuwa a cikin unguwar, jami’an tsaro suka bukaci jama’a da su tsaya a cikin gidajensu sannan kuma su kashe fitilunsu.

Mutanen biyu da ake nema wato Said da kuma Sherif Kouachi, bisa ga dukkan alamu sun ja daga ne a cikin wata madaba’a da ke unguwar.

Shugaba Hollande yace an kai wa kasar hari ne saboda rawar da take takawa wajen yaki da ta’addanci a duniya.

A daidai lokacin da hankulan jama’a suka tashi sakamakon rashin kama wadannan ‘yan bindiga, sai ga wasu bayanai da ke cewa yanu haka wani mutum dauke da nashi makaman, ya yi garkuwa da akalla mutane biyar a wata unguwar da ke cikin birnin Paris.

Binciken farko da jami’an tsaro suka gudanar, na nuni da cewa akwai alaka tsakanin wannan dan bindiga da kuma wadancan mutane biyu da suka kai wa Charlie Hebdo hari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.