Faransa

Ni ma Charlie ne

Masu zanga zangar goyon bayan mujallar Charlie Hebdo
Masu zanga zangar goyon bayan mujallar Charlie Hebdo REUTERS/Francois Lenoir

Ni ma Charlie ne, An kai wa mujallar Charlie Hebdo harin ta’addanci, inda mutane goma sha biyu suka rasa rayukansu, wadanda suka mutu, sun hada da ‘Yan jarida, ‘Yan sanda, da abokai.Da sunan dukkanin kafafen yada labaran Faransa, muna isar da sakon ta’aziyya ga abokan aiki da ‘yan uwan marigaya, sannan muna isar da irin wannan sako ga illahirin ma’aikatan Charlie Hebdo.Muna kallon hakan a matsayin illa ga ‘yancin aikin jarida da na fadin albarkacin baki. Mujallar da ke buga labaran barkwanci, ta kasance wata kafa da ke matukar jan hankulan jama’a.Ayyukanta mujallar sun kasance masu nidashantarwa, sannan suna yaki da wariya da kuma tsatsauran ra’ayi. Mutuwar wadannan mutane ta kasance tafarki na ‘yanci a gare mu. Ba gudu ba ja da baya, ‘yancin yin tunani da kuma fadar albarkacin baki zai ci gaba da kasancewa madogara wajen gudanar da aikinmu.A wannan lokaci na juyayi, muna jaddada cewa ba za mu taba ja da baya saboda barazana ko ta’addanci ba. Ba za mu bari shiru ya rinjaye mu ba, sannan za mu ci gaba da yaki da kowane irin salo na wariya.Kafafen yada labaran Faransa na a cikin shiri domin samar da ma’aikata da kayan aiki domin mujallar Charlie Hebdo ta ci gaba da wanzuwa. Ya zama dole mu tashi tsaye domin kare ‘yancin aikin jarida. Za mu ci gaba da kare wannan ‘yanci da sunan marigayan. Sa Hannu,Christopher Baldelli (RTL), Christophe Barbier (L'Express), Jean-Paul Baudecroux (NRJ), Pierre Bellanger (SKYROCK), Jérôme Bellay (Le Journal du Dimanche), Nicolas Beytout (L’Opinion), Véronique Cayla (ARTE), Matthieu Croissandeau (L’Obs), Nicolas de Tavernost (M6), Bruno Delport (Nova), Louis Dreyfus (Le Monde), Marc Feuillée (Le Figaro), Mathieu Gallet (Radio France), Etienne Gernelle (Le Point), Emmanuel Hoog (AFP), Jean Hornain (Le Parisien),Patrick Le Hyaric (L'Humanité), Gérard Leclerc (LCP-AN), Gilles Leclerc (Public Sénat), Bertrand Meheut (CANAL+), Francis Morel (Les Echos), Denis Olivennes (Lagardère Active / Europe 1), Nonce Paolini (TF1), Fabienne Pascaud (Télérama), Rémy Pflimlin (France Télévisions), Matthieu Pigasse (Les Inrockuptibles), Dominique Quinio (La Croix), Olivier Royant (Paris Match), Marie-Christine Saragosse (France Médias Monde), Jean-Christophe Tortora (La Tribune), Jean-Eric Valli (Les Indés Radio),Maurice Szafran (Le Magazine Littéraire), Alain Weill (NextRadioTV)