Faransa

Hollande ya dawo da farin jininsa ga Faransawa

Shugaban Faransawa Francois Hollande tare da da Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita da  Angela Merkel ta Jamus a gangamin Paris
Shugaban Faransawa Francois Hollande tare da da Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita da Angela Merkel ta Jamus a gangamin Paris Reuters/Philippe Wojazer

Hare Haren da aka kai wa Faransa sun karawa shugaban kasar Francois Hollande farin jini bayan dushewarsa ga Faransawa.  A taron gangamin da aka yi a birnin Paris tagomashin shugaban ya sake dawowa inda Faransawa suka dinga jinjina ma sa, sai dai ba’a san ko hakan zai dore ba.

Talla

Sai dai masana sun ce Faransawa na da saurin mantuwa, domin nan ba da dadewa ba za su iya mantawa da abin da ya faru su koma kan matsalar rashin ayyukan yi da ya addabe su.

Mutane 17 aka kashe a hare haren da ‘Yan bindiga suka kai a cikin kwanaki uku a birnin Paris, lamarin da ya girgiza duniya.

Hollande ya hada gangamin mutane sama da miliyan tare da wasu manyan shugabannin kasashen duniya da suka halarci birnin Paris domin nuna alhini ga Faransawa.

Amma masu sharhin siyasar Faransa suna ganin nan ba da dadewa Faransawa za su manta da Hollande kamar yadda ta faru a lokacin da ya ci yaki a Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.