Jamus

Merkel ta shiga gangamin Musulmi a Jamus

Dubban masu zanga-zangar kyamar Musulunci a Jamus
Dubban masu zanga-zangar kyamar Musulunci a Jamus REUTERS/Fabrizio Bensch

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel da wasu manyan ministocinta za su shiga wani gangami da za a yi a Berlin don samun daidaito da mutunta kowanne addini da shugabanin Musulmin kasar suka kira bayan hare haren da aka kai a Faransa.

Talla

Ana saran gangamin na yau wanda zai samu halartar dmutane da dama a Berlin ya janyo hankalin jama’a kan nuna adawa da tsageranci da kuma ayyukan ta’addancin dake neman zuwa ruwan dare a duniya.

Shugaban kasar Jamus Joachim Gauck na daga cikin wadanda za su yi jawabi ga mahalarta gangamin wanda zai samu halartar mataimakin shugabar gwamnatin Sigmar Gabriel da ministan harkokin waje Frank Walter Steinmeir da wasu manyan jami’an gwamnatin.

Angela Merkel tace Jamus na bukatar zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinin Islama da sauran addinai.

A bangare daya kuma masu yaki da addinin Islama da kuma baki a kasar sun shirya gudanar da wata zanga zanga.

Jamus tana cikin manyan kasashen duniya da ke sahun gaba wajen la’antar hare haren da aka kai wa Mujallar Charlie Hebdo da ta ci zarafin addinin Islama.

Akalla mutane dubu 18 ne suka shiga wata zanga-zangar nuna kyamar addinin musulunci a birnin Dresde da ke gabashin kasar Jamus a makon da ya gabata. Wata kungiya ce mai suna PEGIDA ta jagoranci gangamin inda ta ce wasu na neman musuluntar da al’ummar Turai.

Sai dai masu wannan ra’ayi sun ci karo da turjiya daga wasu Jamusawa masu sassaucin ra’ayi da ke adawa da zanga-zangar a sauran biranen kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.