Ukraine

An yi taron nazarin sasanta rikicin Ukraine

Firimiyan Ukraine Arseni ytseniouk tare da Angela Merkel shugaban gwamnatin Jamus a Berlin.
Firimiyan Ukraine Arseni ytseniouk tare da Angela Merkel shugaban gwamnatin Jamus a Berlin. REUTERS/Hannibal Hanschke

Ministocin harkokin wajen kasashen Ukraine da Rasha da Jamus da Faransa sun yi wani taro a birnin Berlin na kasar Jamus, inda suka duba hanyoyin da za a bi wajen kawo karshen zaman dar dar, da ke barazana ga taron da ake shirin yi don kashe wutar rikicin kasar Ukraine.

Talla

Shugaban Kasar Ukraine Petro Poroshenko na fatan za a iya yin taron na kasashe 4, ranar Alhamis mai zuwa a kasar Kazakhstan, inda za a nemi Rasha ta sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.

Sabuwar yarjejeniyar za ta sanya kasashen Ukraine da Rasha su aiwatar da kudurin zaman lafiyar da aka sanya hannu a kai, cikin watan Satumban bara, wadda ‘yan aware masu goyon bayan Rasha, da dakarun Ukraine suka ki yin aiki da ita a yankin, da tuni ya lakume rayukan kusan mutane dubu biyar.

A karshen makon da ya gabata shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sanar da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da Petro Poroshenko na Ukraine cewa taron ba shi da wani tasiri, in har ba za a yi aiki da yarjejeniyar ba, ita ma Faransa ta bayyana irin wannan damuwar.

Sai dai ministan harkokin wajen kasar Rasha, Sergei Lavrov ya dage kan cewa ba kasashen yammacin duniya ne, za su yi wa Moscow matsin lamba kan yadda za ta yi hulda da Ukraine ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.