Fransa

Kerry ya isa Faransa don jajanta harin Charlie Hebdo

Shugaban Fransa Francois Hollande da Sakataren Wajen Amurka John Kerry
Shugaban Fransa Francois Hollande da Sakataren Wajen Amurka John Kerry

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya isa Faransa, inda ake sa ran yau Juma’a zai gana da Shugaba Francois Hollande wani lokaci a yau.

Talla

Kerry na birnin Paris ne, don kawo karshen kunfar bakin da ake yi kan rashin halartar manyan jami’an Amurka a taron gangamin da aka gudanar domin jajantawa Faransa harin ta’addanci da aka kai wa kasar.

A lokacin da yake ganawa da takransa na Faransa Laurent Fabius, Kerry ya ce kasantuwarsa cikin halin balaguro zuwa wasu kasashe lokacin da aka kai wa Charlie Hebdo hari, da kuma taron gangamin da aka yi wannan ne ya hana shi kasance a Paris wancan lokaci.

Ana sa rai Mr Kerry zai gana da shugaba Hollande kafin yayi jawabi a wani babban zauren dake birnin na Paris.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.