Faransa-Jamus

An dakatar da wata zanga zangar kyamar musulunci a kasar Jamus

'Yan kungiyar PEGIDA suna zanga zanga a kasar Jamus
'Yan kungiyar PEGIDA suna zanga zanga a kasar Jamus REUTERS/Fabrizio Bensch

‘Yan sanda a kasar Jamus sun hana gudanar da wani jerin gwano da aka ce kungiyar nan mai kyamar Musulunci a kasar ta shirya a yankin gabashin birnin Dresden. ‘Yan sanda a yankin na Dresden sun bayyana samun bayannan sirri daga matakin jiha, da na kasa baki daya, cewar kungioyar IS tana shirin kai hari kan kungiyar ta PEGIDA, mai adawa da Musulunci a lokacin zanga-zangar ta yau litinin, abinda suka kira babbar baraza ga tsaron kasar.‘Yan sandan sun ce akwai kiraye-kirayen cewar a kula da wannan batu na zanga-zangar, domin mai yuwuwa  wasu ‘yan kunar bakin wake su shiga ciki domin kai hare-hare a sassan birnin.An dai samu sakwanni ta kafofi daban daban cewar a kyamaci kungiyar PEGIDA ta masu adawa da Musulunci domin su makiya Addinin da kuma Musulmin Duniya ne.A ranar Litinin da ta gabata ma sun shirya zanga-zangar da ta ja hankalin akalla mutane Dubu 25, akan harin da aka kai wa Mujallar Charlie Hebdo ta kasar Faransa.Haka ma a Litinin din da ta gabata, wasu mutane sama da Dubu 10 sun gudanar da zanga-zangar kyamar ita kungiyar ta PEGIDA mai adawa da Musulunci.