Faransa

An cafke wasu ‘yan Chechnya a Faransa

Shugaban Faransa, François Hollande
Shugaban Faransa, François Hollande REUTERS/Philippe Wojazer

Jami’an tsaron kasar Faransa sun kama wasu da ake zargin ‘yan kasar Rasha ne guda biyar, dauke da abubuwan fashewa masu tarin yawa, Sai dai masu gudanar da bincike sun ce har yanzu ba tabbas, ko mutanen suna shirin kai hari ne a cikin kasar.

Talla

Daraktan ‘yan sandan da ke aiki a bangaren sahri’a a birnin Montpellier na kudancin Faransa, Gilles Soulier yace har yanzu ba wata hujjar da ke nuna cewa mutanen suna shirin kai hari.

Ana tsare ne da mutanen, ‘yan asalin kasar Chechnya a kusa da birnin na Montpellier, kuma Soulier ya bayyana lamarin da abin da ke da alaka da adddini.

Tun lokacin da aka kai hari a ofishin mujalar Charlie Hebdo a birnin Paris, kasashen Turai suke ta kai samame kan wuraren da ake gani maboyar wadanda masu tsananin kishin Islama ne.

‘Yan sandan kasar Jamus kusan 200 suna ci gaba da farautar wani gungun masu tsananin kishin addini, da aka ce suna shirin kai hari a a kasar Syria.

Jamusawan sun yi cajin gidaje 13 a birnin Berlin, da ma sauran wurare, inda suke neman mutane da ke da alaka da shugaban wata kungiyar addini, da ake tsare da shi tun ranar juma’a da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.