Faransa

Faransa za ta bayyana shirin yaki da ta’addanci

Firaminstan kasar Faransa Manuel Valls
Firaminstan kasar Faransa Manuel Valls REUTERS/Charles Platiau

Jami’an Gwamnatin Faransa da takwarorinsu na kasashen Turai za su bayyana wani shirin kalubalantar ayyukan ta’addanci da hadin kan juna bayan harin da aka kai birnin Paris inda aka kashe mutane 17. Ana saran Firaminista Manuel Valls zai bayyana sabon shirin kasar na bunkasa tsaro da kuma fuskantar duk wata barazana.

Talla

Kungiyar kasashen Turai za ta tattauna matakan da za ta dauka a birnin Brussels ciki har da shirin biza da ake amfani da shi wajen tafiye tafiye a Nahiyar Turai, tsarin da wasu kasashe ke suka tsaurara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.