Ingila-IS

Ana taron IS a London

Zauren taron tattauna barazanar Mayakan IS a London
Zauren taron tattauna barazanar Mayakan IS a London REUTERS/Peter Nicholls

Manyan Jami'an diflomasiyar kasashen Turai daga kasashe 21 na duniya sun kaddamar da tattaunawa ta musamman a London dangane da mayakan IS masu da’awar jihadi a Iraqi da Syria. Taron ya hada mambobin kasashe 21 daga cikin 60 da suka amince da daukar matakan Soji akan kungiyar IS da ta karbe ikon wasu yankuna a kasashen Syria da Iraqi.

Talla

Daga cikin mahalartan taron akwai Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, da Firaiministan kasar Birtaniya David Cameron.

Wannan shi ne karon farko da kasashen suka hadu karkashin jagorancin Amurka domin shirya yadda za su yi fada da kungiyar ta IS.

Kasashen sun ce za su ci gaba da tattaunawa anan gaba game da yadda za su kawo karshen barazanar ta’addanci a kasashensu.

Hukumar ‘Yan sanda ta Turai tace sama da ‘Yan kasashen Turai 5,000 ne suka tafi yaki domin taimakawa mayakan IS a Iraqi da Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.