Ukraine

Sojojin Ukraine sun fice tashar jirgin Donetsk

Tashar Jirgin sama na Donetsk a Ukraine
Tashar Jirgin sama na Donetsk a Ukraine REUTERS

A kasar Ukraine, Cikin sa’o’I 24 an kashe Sojoji 41 da fararen hula 24 a barin wutar da aka yi tsakanin ‘yan tawaye da Sojojin gwamnatin kasar a Donetsk. Yanzu haka Sojojin Ukraine sun fice tashar jirgin saman Donestk da ‘Yan yawaye suka kwace. Kuma a yau watanni 9 ke nan aka kwashe ana rikici a Ukraine.

Talla

Tun a safiyar Laraba ne ake musayar wuta tsakanin ‘Yan tawayen Ukraine da Sojojin gwamnati.

Kuma adadin Sojoji  41 aka kashe da fararen hula 24, cikinsu kuma akwai mutane 13 da a yau Alhamis aka kashe bayan da wani harin makamin roka ya tarwatsa mota kirar bus da suke ciki a tsakiyar Donetsk.

Ma’aikatar tsaron Ukraine tace sojojnta sun fice tashar jingin sama da ke hannun ‘Yan tawaye. Amma sojojin sun karbe ikon wasu yankuna na birnin Donetsk.

Wannan dai na zuwa bayan wani taro a Berlin tsakanin Faransa da Jamus da Rasha da Ukraine wadanda suka amince a kawo karshen fada tare da janye muggan makamai.

Yau tsawon watanni 9 ke nan ana rikici a kasar Ukraine, kuma a jiya Shugaban kasar Poroshenko ya yi zargin cewa akwai dakarun Rasha sama da 9,000 da ke taimakawa ‘Yan tawaye da suka karbe ikon gabacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.