Bakonmu a Yau

Dakta Isah Abdullahi na Jami'ar Gombe

Sauti 03:34
Shugabar Asusun Lamunin na Duniya Christine Lagarde
Shugabar Asusun Lamunin na Duniya Christine Lagarde REUTERS/Gary Cameron/Files

Shugabar Asusun Lamuni na Duniya IMF Christine Lagarde, ta yi gargadin cewa abu ne mai wuya kasar Girka ta fita daga cikin matsin tattalin arziki bayan kammala zabe a ranar lahadi mai zuwa. Girka dai ta jima tana fama da matsalar tattalin arziki, lamarin da ya sa Bankin Duniya da kuma Kungiyar Tarayyar Turai suka taimaka ma ta da kudade a matsayin rance sau da dama amma har yanzu ba wani takamaiman sauyin da aka gani. Abdurrahman Gambo Ahmad ya zanta da Dr Isa Abdullahi na jami’ar tarayya da ke Kashere jihar Gomben Najeriya kan wannan batu.