EU-Najeriya

EU ba za ta tura wakilai ba a arewa maso gabacin Najeriya

Yankin arewa maso gabacin Najeriya mai fama da matsalar tsaro
Yankin arewa maso gabacin Najeriya mai fama da matsalar tsaro Reuters/Stringer

Kungiyar Tarayyar Turai ta EU ta ce ba za ta tura masu sa ido zuwa yankin arewa maso gabacin Najeriya ba, a zaben gama gari da za a gudanar a a kasar saboda matsaloli na tsaro a yankin. A ranar 14 ga watan Fabrairu ne yan Najeriya za su shiga runfunan zabe, don kada kuri’ar zaben Shugaban kasa da na ‘yan Majalisu.

Talla

Jagoran tawagar masu sa ido karkashin kungiyar ta EU Ambasada Santiago Fisas, yace za su kaucewa yankin ne saboda matsalolin tsaron da ake fuskanta.

Fisas ya ce tun cikin watan Nuwamban shekarar da ta gabata masu sa idon suka isa Najeriya, inda suka fara da duba yadda jam’iyyun kasar suka gudanar da zabukansu na fidda gwani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.