Faransa

Faransa ta kame wasu mutane 5 da ake zargi 'yan ta'adda ne

Shugaban Faransa, François Hollande
Shugaban Faransa, François Hollande Crédit ?

A Faransa, jami’an tsaro sun yi nasarar cafke wasu mutane biyar da ake zargin ‘yan ta’ada ne a garin Lunnel dake kudanci kasar.An kame mutanen ne lokacin da jami’an tsaro suka kai wani samame a garin na Lunnel, da nufin murkushe wani gungun masu tsanani kishin Islama.Rahotani dake futowa daga garin na Lunnel sun tabbatar da cewa sojan Faransa sun yi nasarar kame wasu mutane biyar da ake zargin suna da alaka da ‘yan kungiyar ISIS, ta masu tsananin kishin Islama dake gudanar da ayyukanta a kasashen Iraqi da Syria.Mininstan cikin gidan kasar Bernard Cazeneuve, yace garin na Lunnel dake da al’umar data kusan dubu 26, da kuma ke gab da garin Montpellier, na daya daga cikin yankunan da hukumomin Faransa suka sakawa ido ministan.Cazeuneuve ya bayyana matsayar da Gwamnatin Faransa ta cima, na ganin ta murkushe duk wata barazana daga yan ta’ada a cikin kasar.Ministan yace tun bayan harin da ‘yan ta’ada suka kai a kasar, jami’an tsaro na cikin shirin ko ta kwana, kuma ba yadda za a cima wanan nasara sai da hadin kan al’umar, tareda bayar da rahotani cikin lokaci.