Ukraine-Rasha

Amurka ta shirya karawa Rasha Takunkumi

reuters.com

Sakataren Baitul-Malin kasar Amurka Jack Lew ya ce kasar ta Amurka, ta shiryawa karawa kasar Rasha Takunkumin karya tattalin arziki akan yanda take ci gaba da taka rawar hanawa kasar Ukraine ‘yancin kanta

Talla

Sai dai Sakataren ya bayyana cewar yanzu abin da suka baiwa fifiko shi ne sasantawa a cikin Ruwan sanyi, idan Rashar ta ci gaba da kafewa, to lokacin ne za su yi gaban kansu.

Yace sun shirya kara kuntatawa kasar Rasha akan wannan lamari na kasar Ukraine idan bukatar yin hakan ta taso, amma yanzu za su ci gaba da matsa mata lamba tare da sauran kasashen kungiyar tarayyar Turai.

Kasar Rasha dai ta ci gaba da musanta laifin taimakawa ‘yan tawayen gabashin Ukraine da kasashen na yammacin Duniya ke mata, amma a wurinsu, Rasha dai na wasa da hankalinsu ne kawai.

Amurka dai na bukatar Rasha ta sauya manufarta ne ta yin babakere a yankin gabashin kasar Ukraine, kamin ita da sauran kasashen Turawan su sauwaka mata a matakin kangeta da suke ci gaba da dauka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.