Ukraine-Rasha

Gobe za a ci gaba da taron sasanta rikicin kasar Ukraine

'Yan tawayen kasar ukraine, masu goyon bayan Rasha
'Yan tawayen kasar ukraine, masu goyon bayan Rasha REUTERS/Alexander Ermochenko

Gobe juma’a ake sa ran ci gaba da wani zagayen tattaunawar zaman lafiya, da ake yi don kawo karshen rikicin kasar Ukraine. Za a yi ganawar ne a Minsk, babban birnin kasar Belarus, wadda zata sami halartar wakilan kungiyar Hadin kan kasashen Turai da na Rasha.Cikin wata sanarwar da ta fitar, ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Belarus ta fitar tace, hukumomin Ukraine sun bayyana aniyar gudanar da taron sasanta rikicin gobe juma’a.Sanarwar na zuwa ne jim kadan bayan da shugaban kasar ta Ukraine Petro Poroshenko ya nemi a gaggauta ganawa da ‘yan awaren masu goyon bayan Rasha, don kawo karshen zub da jinin da ake yi a gabashin kasar.Poroshenko yace yana fatan taron zai kawo karshen rikicin cikin gaggawa, tare da janye muggan makaman da aka girke a yankin, kamar yadda aka tsara a wata yarjejeniyar ta watan Satumba.A makon daya gabata jagoran ‘yan tawayen ya fice daga wata tattauanawar, ya kuma bayar da sanarwar ci gaba da kai hare hare, don kama wasu karin yankunan.Taron da aka yi ranar 24 ga watan Disamba a birnin na Minsk ya gagara samar da wata mafita kan kan rikicin na Ukraine, inda jin kadan da gudanar da shi wani sabon rikicin ya barke.