Birtaniya

Birtaniya za ta amince da Dokar haifar yara ga Iyaye Uku

uk.news.yahoo.com

‘Yan majalisar dokokin kasar Britaniya na shirin kada kuri’a, don amincewa da wani tsarin da zai bawa Iyaye Uku damar haifar Yara. Sai dai masu adawa da tsarin, da kuma shugabannin addini sun bayyana kyamarsu ga tsarin  

Talla

Tsarin da ake kira Mitochondrial DNA Donation a turance, na bayar da damar samar da kwayoyin hallita ga dan tayin da mahaifiyarshi ke da wata cutar da zai iya gado.

Ana bayar da gudumwara ne ga matan da ake fargabar cewar ‘ya‘yansu za su iya kamuwa da cutuka kamar su ciwon Suga, da rashin gani sosai.

A karkashin tsarin IVF, da ake neman ya zama Doka, baya ga samun kwayoyin hallita daga Uwa da Uba, dan tayin zai kuma iya samun gudunmawar wasu kwayoyin halitta masu lafiya daga wata Macen daban.

Tuni aka fara tafka muhawara tsakanin masu goyon baya da masu adawa da tsarin, da suke gani zai bude Kofa ga masu neman sarrafa Jarirai don sayarwa.

To sai dai kuma wasu na ganin zai taimaka wa matan kasar ta Britaniya kimanin Dubu 2 da 500, da ke cikin kasadar gadon miyagun cutuka ga ‘ya‘yansu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI