Manyan jami'an Rasha da na Nato sun gana a birnin Munich
Karon farko a cikin watanni 10 a wannan asabar an gana tsakanin ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov da kuma Sakataren kungiyar tsaro ta Nato Jen Stoltenberg a birnin Munich na kasar Jamus.
Wallafawa ranar:
Duk da cewa ba a yanke alaka a hukumance tsakanin kungiyar da kuma Rasha ba, to sai dai tun lokacin da mazauna yankin Crimea suka jefa kuri’ar ballewa daga Ukraine ne alaka ta yi tsami tsakanin bangarorin biyu.
Mutanen biyu dai na harlartar taron Duniya kan tsaro ne da ke gudana a birnin Munich, wanda kasashen Jamus, Faransa, Rasha, Ukraine da kuma Isra’ila, yayin da Turkiyya ta kaurace wa taron saboda an gayyaci Isra’ila.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu